Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Bellerin, James, Kante, Castagne, Partey, Doucoure
Mahaifin dan wasan Barcelona Lionel Messi ya isa Sufaniya domin tattaunawa da da shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu kan makomar dan wasan na Argentina, a cewar jaridar Sky Sports.
Messi, mai shekara 33, ya amince da kwangilar shekara biyar da City Football Group a kan £623m inda zai kwashe kakar wasa uku a Manchester City sannan ya tafi New York City FC. (Record)
Paris St-Germain ta yi tayin biyan £25m da kuma ƙarin £5m kuɗin talla kan ɗan wasan Arsenal Hector Bellerin, a yayin da Bayern Munich daJuventus su ma suke zawarcin ɗan wasan na Sufaniya mai shekara 25. (Guardian)
Everton ta amince ta ɗauko ɗan wasan Colombia James Rodriguez, 29, daga Real Madrid a kwangilar shekara uku. (Telegraph)
Chelsea za ta sayar da N'Golo Kante kan £80m a yayin da Inter Milan take zawarcin ɗan wasan na Faransa mai shekara 29. (Express)
Sai dai tsohon ɗan wasan Leicester Kante yana son ci gaba da zama a Chelsea. (Goal)
Leicester ta amince da yarjejeniyar £22m domin ɗauko ɗan wasan Belgium Timothy Castagne, mai shekara 24, daga Atalanta. (Telegraph)
Ɗan wasan Atletico Madrid Thomas Partey, mai shekara 27, yana son tafiya Arsenal sai dai Gunners na bukatar sayar da wasu 'yan wasa kafin ta sayi ɗan wasan na Ghana kan £44.5m. (Goal)
Monaco ta bayyana aniyarta ta sayo ɗan wasan WatforddaFaransa Abdoulaye Doucoure bayan Everton ta gaza sayensa. (Evening Standard)
KocinTottenham Jose Mourinho ya shirya sayar da ɗan wasan Faransa mai shekara 23 Tanguy Ndombele. (Sun)
Newcastle na yunkurin gyara yarjejeniyar dauko dan wasan Bournemouth Callum Wilson, mai shekara 28, a yarjrjniyar da za ta kai ga mika wa Cherries dan wasan Scotland Matt Ritchie, amma Aston Villa tana son dauko dan wasan na Ingila. (Sky Sports)
PSG ta tuntubi dan wasan Inter da Slovakia Milan Skriniar, mai shekara 25, wanda Tottenhamtake zawarci.(Calciomercato - in Italian)
Crystal Palace ta ki amincewa da tayin da RB Leipzig na bayar da £20m don dauko dan wasan Norway Alexander Sorloth, mai shekara 24. (Mail)
Juventus tana son dauko dan wasan Barcelona da Uruguay Luis Suarez, mai shekara 33, ko kuma dan wasan Roma da Bosnia Edin Dzeko, mai shekara 34. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Golan Sufaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, ya shriya ci gaba da zama a Chelsea inda zai yi gumurzu don samun wurin zama, ko da kuwa kungiyar ta dauko sabon gola. (Telegraph)
Al Nassr ta yi tayin ba da euro 20m ga dan wasan ArsenalMesut Ozil, mai shekara 31, domin ya koma murza leda a Saudiyya. (Fanatik - in Turkish)