Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ivan Rakitic: Sevilla ta sayi dan wasa da a baya ta sayar wa Barcelona
Sevilla ta kara sayan dan wasan tsakiyarta dan kasar Crotia Ivan Rakitic da a baya ta sayer wa abokiyar burminta ta La Liga Barcelona.
Dan wasan ya sanya hannu kan kwantaragin shekara hudu da kungiyar Sevilla wadda ta lashe kofin Europa.
Dan shekara 32, wanda ya zauna a Sevilla tsakanin watan Junairun shekarar 2011 da Yunin 2014 kafin ya koma Barcelona, ya dauki kofi 13 a Nou Camp, ciki har da na La Liga hudu da Champios daya.
A wata sanarwa da Barcelona ta fitar: "Kungiyar ta Andalus za ta biya FC Barcelona yuro miliyan 1.5 sannan kuma ta biya wasu yuro milyan 9 bisa wata yarjejeniya ta gaba."