Lionel Messi:Shugaban Argentina na son dan wasan ya koma gida, Chelsea ta amince ta sayi Havertz

Shugaban Argentina, Alberto Fernandez, ya roki Lionel Messi ya koma kasarsa domin kammala sana'arsa ta kwallon kafa a kungiyarsa ta farko Newell's Old Boys, a cewar jaridarC5N, wacce ta ambato Evening Standard.

Messi zai bar Barcelona a bazarar nan kuma"akwai yiwuwar" ya tafi Manchester City, a cewar mutumin da ke takarar shugabancin Barcelona Toni Freixa. (Goal)

Barcelona ta yi amannar cewa hanya daya kawai da dan wasan na Argentina, mai shekara 33, zai iya barin kungiyar ba tare da ya biya kudi ba ita ce ya yi alkawarin ba zai murza leda ba a kakar wasa mai zuwa. (ESPN)

Chelsea ta amince ta sayi dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, a kan £72m, kuma hakan zai sa kudin da za su kashe a kasuwar 'yan kwallo a bazara ya zarta £200m. (Guardian)

Manchester United na zawarcin dan wasan RB Leipzigda Faransa Dayot Upamecano, mai shekara 21. (ESPN)

Dan wasan Sufaniya Dani Ceballos, mai shekara 24, zai koma Arsenal don zaman aro na kakar wasa daya daga Real Madrid a wannan makon. (Guardian)

Kungiyoyin kwallon kafa a Saudiyya da Qatar sun bayyana sha'awar dauko dan wasan Jamus Mesut Ozil a bazarar nan, sai dai dan wasan na Arsenal, mai shekara 31, ba shi da niyyar barin London. (Telegraph)

Tottenham ta soma tattaunawa don sabunta kwangilar golan Faransa Hugo Lloris, mai shekara 33, duk da cewa ta dauko Joe Hart. (Football Insider)

Kazalika Tottenhamna tattaunawa domin dauko dan wasan Bournemouth da Norway Josh King da kuma Callum Wilson, dukkansu masu shekara 28. (Talksport)

Aston Villa na zawarcin Wilson daga Bournemouth. (Mail).