Champions League: Hotunan yadda PSG da Bayern Munich ke atisaye

Ranar Lahadi PSG za ta kece raini da Bayern Munich a wasan karshe na Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Za a yi kece raini wasan ƙarshe na Champions League tsakanin PSG da Bayern Munich

Paris Saint-Germain da ta kai wasan ƙarshe karon farko a tarihi a gasar Zakarun Turai ta Champions Leagus na shirin fafatawa da Bayern Munich a ranar Lahadi a Lisbon.

Babban wasa ne da zai ja hankalin duniya tsakanin manyan ƙungiyoyin na Turai guda biyu - waɗanda ba su saba shan kashi ba.

Amma za a yi fafatawar ne ba tare da 'ƴan kallo ba a filin Benfica a Lisbon saboda cutar korona.

PSG za ta iya kasancewa ƙungiya ta biyu daga Faransa da ta taɓa lashe kofin gasar bayan shekaru 27 da Marseille ta lashe kofin na Champions League.

Karo na 11 kenan da Bayern ta kai zagayen ƙarshe a gasar, inda ta lashe kofi biyar kuma na baya-bayan nan shi ne a 2013.

Idan dai har PSG ta lashe kofin, zai ƙara ɗaga martabarta a cikin sahun manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na turai musamman kuma zaratan 'ƴan wasanta Neymar da Kylian Mbappe.

PSG tun watan Nuwamba sau ɗaya aka doke ta.

Sai dai Bayern Munich na harin lashe kofi na uku ne a bana bayan ta lashe Bundesliga da kofin Jamus, kuma wasanni 29 ta buga ba a doke ta ba inda ta lashe dukkanin wasanninta 10 a Champions League a bana.

Hankali zai koma ga Robert Lewandowski a tawagar Bayern Munich wanda ya ci kwallaye 55 a kakar bana

Ga yadda Bayern Munich da Paris Saint-Germain ke atisaye

Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images

Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images

Bayern Munich

Asalin hoton, @FCBayernEN

Bayern Munich

Asalin hoton, @FCBayernEN

Bayern Munich

Asalin hoton, @FCBayernEN

Yadda ƴan wasan PSG ke shirin haɗuwa da Bayern Munich

PSG

Asalin hoton, Getty Images

PSg

Asalin hoton, Getty Images

PSG

Asalin hoton, Getty Images

PSG

Asalin hoton, Getty Images

PSG

Asalin hoton, @PSG_English

PSG

Asalin hoton, @PSG_English

PSG

Asalin hoton, @PSG_English

PSG

Asalin hoton, @PSG_English