Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Saul, Pogba, Dybala, Oblak, Winks, Jimenez

Manchester United ta shirya ba da kwangilar dogon lokaci ga dan wasan Sufaniya wanda farashinsa ya kai £70m Saul Niguez, mai shekara 25, kuma za ta rika biyansa £150,000 duk mako idan ta dauko shi daga Atletico Madrid a bazarar nan, in ji jaridar Star.

Manchester United tana duba yiwuwar yin musayar 'yan wasa inda za ta bai wa Juventus dan wasan Faransa Paul Pogba, mai shekara 27, sannan ta karbo dan wasan Argentina Paulo Dybala, mai shekara 26. (Tuttosport - in Italian)

BurinChelseana dauko golan Atletico Madrid Jan Oblak, mai shekara 27, ya samu tagomashi a yayin da rahotanni suka ce kungiyar da ke buga La Liga tana son maye gurbin dan kasar ta Slovenia. (Football London)

Manchester City na shirin kashe £40m don dauko dan wasan Ingila daTottenham Harry Winks, mai shekara 24. (Sun)

Cristiano Ronaldo yana so Juventus ta sayo dan wasan Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29, daga Wolves domin su zama 'yan wasan gaba tare a kakar wasa mai zuwa. (La Gazzetta dello Sport, via Express)

Lille ta ki karbar euro 20m daga Everton kan dan wasan da ke tsaron baya Gabriel, mai shekara 22, saboda sun kulla yarjejeniyar sayar da shi ga Napoli, duk da cewa Arsenal da Manchester United sun nuna sha'awar dauko dan wasan na Brazil. (Gianluca di Marzio)

Newcastle na son dauko dan wasan Manchester United Chris Smalling, mai shekara 30, wanda ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Roma. (Newcastle Chronicle)

Golan Arsenal Emiliano Martinez ya ce kungiyoyin kwallon kafar Turai 10 suna zawarcinsa bayan rawar ganin da dan wasan na Argentina mai shekara 27 ya taka a kakar wasan da ta wuce. (Marca - in Spanish)

West Brom da West Ham suna zawarcin dan wasan Brazil Junior Caicara, mai shekara 31, wanda ke murza leda a kungiyar Istanbul Basaksehir. (Sun)

Inter Milan za ta iya dauko dan wasan Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, daga Barcelona, a cewar tsohon shugaban kungiyar da ke buga gasar Serie A Massimo Moratti. (Quotidiano)

KazalikaInter na son dauko dan wasan Chelsea da Faransa N'Golo Kante, mai shekara 29. (La Gazetta dello Sport - in Italian)

Sabon kocin Newcastle Steve Bruce yana tattaunawa da Matty Longstaff da zummar rarrashin dan wasan mai shekara 20 ya sabunta zamansa. A watan nan kwangilar dan wasan na Ingila ta kare kuma kokarin sabunta ta ya gamu da cikas. (Star)