Blaise Matuidi: ya koma kungiyar da Beckham ne ke da ita Inter Miami

Dan wasan tsakiya dan kasar Faransa Blaise Matuidi ya zama fitaccen dan kwallo na farko da kungiyar Inter Miami da ke buga Lig Soccer ta fara dauka.

Matuidi da kungiyarsa ta Juventus wadda ita ce gwarzuwar gasar Italiya sun amince su kawo karshen kwantiraginsa da suka cimma a ranar Laraba.

Dan shekara 33 wanda ya lashe kofin duniya da Faransa a 2018 - ya buga kwallo da mai kungiyar Inter Miami David Beckham a Paris St-Germain kafin ya koma Juventus a 2017.

"Ina fatan mu lashe gasa mai waya tare." In ji Matuidi "Wannan ba karamin kalubale ba ne gare ni."

Kungiyar ta Inter Miami ta yi rashin nasara a duka wasanni biyar din da ta buga na farkon kaka, wadda aka shirya ci gaba da bugawa a ranar 22 ga watan Agusta.

"Zan yi matukar murna na tarbar abokina Blaise zuwa Inter Miami," In ji Beckam, tsohon dan wasan Manchester United.

"Abin jin dadi ne kuma babban dan wasa ne kamar kyauta ne garemu. Samun wanda ya ci kofin duniya a sabuwar kungiyarmu ba karamin abin alfahari ba ne - a wajena ni mai kungiyar da kuma magoya bayanmu.

Matuidi wanda zai sanya riga lamba takwas, ya lashe kofi bakwai cikin kaka takwas da ya buga a baya - sau hudu a Faransa da PSG sai kuma sau uku a Italiya da Juventus - kuma da shi aka ci Crotia 4-2 a wasan karshe na cin kofin duniya.