Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Coutinho, Willian, Ter Stegen, Rodriguez, Aurier, Watkins, Benrahma
Jaridar (Sport ta ruwaito cewa tattaunawar da dan wasan Barcelona Philippe Coutinho yake yi domin yiwuwar tafiya Arsenal "ta yi nisa". Dan wasan na Brazil mai shekara 28 ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Bayern Munich.
Arsenal ta yi tayin bayar da kwangilar shekara uku ga dan wasan Chelsea daBrazil Willian, mai shekara 31, a cewar (Sky Sports).
An samu ci gaba a tattaunawar daChelsea take yi da dan wasan Real Madrid Sergio Reguilon, mai shekara 23, wanda ya kwashe kakar wasan da ta wuce yana zaman aro a Sevilla. (ESPN)
Golan Barcelona Marc-Andre ter Stegen yana shirin sanya hannu a kan sabuwar kwangilar shekara biyar a kungiyar. Matakin zai bata ran Chelsea, wadda ta dade tana sanya ido a kan dan wasan na Jamus mai shekara 28 da zummar dauko shi. (Mundo Deportivo via Sun)
Dan wasanReal Madrid James Rodriguez, dan shekara 29, yana son tafiya Atletico Madrid a kan £13.5m. (El Golazo de Gol via Sun)
Tottenham ta shirya sayar da dan wasan da aka yi wa farashi £35m Serge Aurier, kuma AC Milan daMonaco suna son dauko dan kasar ta Ivory Coast. (Mirror)
Werder Bremen tana son karbo aron dan wasan Manchester Uniteddan shekara20 Tahith Chong. (Bild - in German)
Fulham za ta sabunta kwangilar kocintaScott Parker. (Express)
Tottenham na sanya ido kan dan wasan Brentford da Algeria Said Benrahma, mai shekara 24. (Mirror)
Crystal Palace ta yi tayin dauko dan wasan Scotland Ryan Fraser. Dan wasan mai shekara 26 ba shi da kungiya tun da ya bayar Bournemouth. (Guardian)
Jason Tindall, mai shekara 42, yana cikin masu fafatawa don maye gurbin Eddie Howe a matsayin kocinBournemouth. (Telegraph)
Tottenham ta amince ta sayar da dan wasan AmurkaCameron Carter-Vickers, dan shekara 22, a kan £2.5m. (Football Insider)