Real Madrid: Ko kun san Iker Casillas ya lashe kofi 16?

Tsohon mai tsaron ragar Real Madrid, Iker Casillas, mai shekara 39 ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa.

Casillas ya buga wa Real Madrid wasa 725 a kaka 16 da ya yi a Santiago Bernabeu, inda ya lashe Champions League uku da kofin La Liga biyar.

Ya kuma bayar da gudunmawar da ta kai tawagar kwallon kafar Spaniya ta ci kofin duniya a 2010 da kofin Nahiyar Turai biyu; a 2008 da kuma 2012.

Casillas ya koma FC Porto da taka leda a 2015, sai dai bai kama gola ba tun da ya kamu da ciwon bugun zuciya a lokacin atisaye a watan Afirilun 2019.

A lokacin da yake jinya an ba shi aikin koci da zai yi tare da masu horas da kungiyar a Yulin 2019.

Dan wasan ya kama gola sau 256 a kungiyar Porto, ya kuma lashe kofin Premier na kasar ta Portugal.

Casillas ya buga wa tawagar Spaniya wasa 167 tsakanin shekarun 2000 zuwa 2016, kuma Sergio Ramos ne kadai ke da yawan buga wa Spaniya tamaula fiye da shi.

Real Madrid ta ce Casillas, wanda ya koma Bernabeu da tsare raga a lokacin yana da shekara tara da haihuwa, babu golan da ya kai shi kwazo a tarihin kungiyar na tsawon shekara 118.

Cikin watan Fabarairu, Casillas ya bayyana shirinsa na takarar shugaban hukumar kwallon kafar Spaniya, daga baya ya janye sakamakon matsanancin yanayi da kasar ta shiga saboda bullar cutar korona.

Tarihin tamaular Iker Casillas

An haifi Iker Casillas Fernandez ranar 21 ga watan Mayun 1981 a Mostoles, Spaniya.

Tsohon Golan Real Madrid da Porto ya lashe kyautar mai tsaron raga da babu kamarsa ta IFFHS karo biyar tsakanin 2008 zuwa 2012.

Yadda ya fara Tamaula

Casillas ya fara kwallo tun yana dan karami kuma a kungiyar da yake kauna Real Madrid tun daga 1990.

Tun daga nan ya mayar da hankali kan yadda zai zama kwararren mai tsara raga ya dunga sa kwazo, hakan ya sa tawagar Spaniya ta matasa 'yan shekara 15 ta gayyace shi a 1996, wasa daya kacal ya kama daga nan ya koma ta matasa 'yan shekara 16.

A nan ne ya nuna kansa da ya sa Real Madrid ta fara amfani da shi a karamar kungiyar wato Real Madrid C.

A shekarar 1999 ya shiga jerin fitattun 'yan kwallon Turai 11 na Champions League, kuma ya zama matashin da ya tsare raga mai shekara 18 da wata shida a ranar 15 ga watan Satumba a fafatawa da Olympiakos.

Fara wasanni

Iker Casillas ya fara buga wa tawagar kwallon kafar Spaniya wasa a Yunin 2000 a karawa da Sweden a wasan da suka tashi 1-1.

Ya fara tsaron ragar Real Madrid a gasar La Liga ranar 18 ga watan Satumbar 1999 a wasan da suka tashi 2-2 da Athletic Bilbao.

Nasarorin da ya samu

A Real Madrid ya ci kofi 16

  • 3 European Cups,
  • 3 Kofin Zakarun nahiyoyin duniya, Club World Cups
  • 2 European Super Cups
  • 5 Spanish La Liga
  • 2 Copa del Rey
  • 4 Spanish Super Cups

A Portugal tare da Porto

  • 2 Kofin gasar Portugal
  • 1 Supercup.

A tawagar kwallon kafar Spaniya

  • Ya buga mata wasa 167
  • Ya lashe kofin duniya daya
  • Kofin nahiyar Turai biyu
  • Kofin duniya na matasa 'yan kasa da shekara 20