Ballon d'Or: A bana ba za a bayar da kyautar zakaran kwallon kafa ba

Karon farko a tarihi, ba za a gudanar da bikin bayar da kyautar zakaran kwallon kafa na duniya ba a bana, wadda ake kira Ballon d'Or.

Mujallar kwallon kafa ta kasar Faransa wadda ke bayar da kyautar ta Ballon d'or duk shekara, ta ce babu yadda za a yi adalci wajen bayar da kyautar a bana ganin cewa akwai wasu kasashe da ba su kammala gasarsu ba saboda annobar korona.

A bara dan kwallon Argentina da ke murza leda a Barcelona, Lionel Messi ne ya lashe kyautar a yayin da Megan Rapinoe ta Amurka ta samu kyautar a bangaren mata.

Annobar Korona ta tilasta dakatar da kwallon kafa a duk fadin duniya a cikin watan Maris kuma kuma sai a cikin watan Mayu aka koma taka leda inda gasar Bundesliga ta Jamus ta sharewa sauran hanya.

Wannan ne karon farko da ba za a gudanar da bukin karamma dan kwallo mafi bajinta ba tun daga aka soma bada kyautar ballon dor a shekarar 1956.

Mujallar kwallon kafar ta Faransa ta ce a yanzu za ta mayar da hankali ne wajen shirya bikin da za a gudanar da shekara ta 2021.