Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Grealish, Sergi Roberto, Hojbjerg, Ivanovic, Lewis
Aston Villa za ta sabunta kwangilar kyaftin dinta Jack Grealish, mai shekara 24, inda za ta rika biyansa £100,000 duk mako a yayin da Manchester United take zawarcinsa. (Sun)
Manchester City ba ta tuntubi Barcelona ba kan dan wasanta na baya Sergi Roberto, duk da rahotanni masu karfi da ke cewa tana son dauko dan wasan na Sufaniya mai shekara 28 - kuma ba ta da shirin zawarcinsa. (Manchester Evening News)
Liverpool na dab da kammala kulla yarjejeniyar £9m don dauko dan wasan Real Betis da Algeria Aissa Mandi, dan shekara 28. (Bein Sports via Daily Mail)
Kazalika Liverpool na shirin biyan £10m don karbo dan wasan Norwich da Arewacin Ireland Jamal Lewis, mai shekara 22, a yayin da take neman wanda zai maye gurbin Andy Robertson. (Daily Mirror)
Dan wasan Southampton dan kasar Denmark Pierre-Emile Hojbjerg, mai shekara 24, na shirin tafiya Tottenham a kan £15m, yayin da shi kuma Kyle Walker-Peters, dan shekara 23, zai tafi Southampton a kan £12m. (Telegraph)
Tsohon dan wasan Chelsea Branislav Ivanovic ya ce watakila zai tafi Everton don yin aiki tare da tsohon mai gidansa Carlo Ancelotti.(Sun)
Liverpool, Crystal Palace da kuma Wolves sun nuna sha'awar dauko dan wasan Watford dan kasar Senegal mai shekara 22 Ismaila Sarr. (Watford Observer)
Leicester City tana son bai waBarcelona aron dan wasan Portugal mai shekara 20 Francisco Trincao don ya yi zaman kakar wasa biyu, amma tana so Barca ta tabbatar da cewa za ta saye shi kan £45m idan wa'adin zamansa ya kare. (Guardian)
Everton ba za ta sayi dan wasan da ke da suna irin nata ba Everton a yayin da dan wasan na Brazil, dan shekara 24, ya shirya tsaf don tafiya Benfica daga Gremio. (Goal)
Southampton na son dauko dan wasan da ke tsaron baya Deyovaisio Zeefuik, mai shekara 22, sai dai dan kasar ta Netherlands ya gwammace ya tafi Jamus. (Southern Daily Echo)
Tsohon dan wasan Manchester United Angel Gomes, dan shekara 19, ya tafi Lille inda ya sanya hannu kan kwangilar sekara biyar bayan ya bar Old Trafford a bazarar nan. (Metro)
Newcastle na son dauko dan wasanBournemouth dan kasar Norway Josh King, mai shekara 28, da kuma dan wasan Wales David Brooks, dan shekara 23. (Telegraph).