Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United na son ɗauko Coman, Napoli ta amince ta biya euro 60m kan Osimhen
Manchester United na sha'awar dauko dan wasan Faransa daBayern Munich Kingsley Coman, mai shekara 24. (Athletic - subscription required)
Napoli ta amince ta biya euro 60m don sayo dan wasan Lille da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 21. (Guardian)
Everton da Leeds United suna son dauko golan Manchester United da Argentina Sergio Romero, mai shekara 33, wanda yake korafi saboda an mayar da shi kurar baya a Old Trafford. (ESPN)
Barcelona ta matsu sosai ta sabunta kwangilar Ansu Fati, mai shekara 17, domin hana shi tafiya Manchester United. (Sport)
Tsohon kyaftin na Tottenham Ledley King yana tattaunawa da kungiyar domin yin aiki da Jose Mourinho a tawagar masu horas da 'yan wasa. (Telegraph)
West Ham na kara himma a yunkurin dauko dan wasan Brentford da Algeria Said Benrahma, mai shekara 24. (Times - subscription required)
Roma ta wallafa hoton dan wasan da take aro Chris Smalling, mai shekara 30, sanye da rigar da za su buga kwallo a kakar wasan badi kuma tana da kwarin gwiwar sayen dan wasan na Manchester United da Ingila. (Corriere dello Sport - in Italian)
Manchester United ba za ta tsawaita yarjejeniya daRoma ba kan Smalling ko kuma yarjejeniyarsu da Inter Milan kan dan wasan Chile Alexis Sanchez, mai shekara 31, domin kuwa tana so 'yan wasan su koma can a matsayin mallakin kungiyoyin baki daya. (Sky Sports)
Brighton ta taya dan wasan Paderborn da Jamus da ke buga gasar 'yan kasa da shekara 20 Luca Kilian, wanda kuma AC Milan da Freiburgsuke son dauka. (Mail)
Real Madrid na fatan tara euro 180m a bazarar nan idan suka sayar da wasu 'yan wasa cikinsu har da - dan wasan Wales Gareth Bale, mai shekara 31, da wasan Colombia James Rodriguez, mai shekara 29, da kuma dan wasan Serbia Luka Jovic, mai shekara 22. (Marca).