Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Valencia ta ƙi rage farashin Torres, Chelsea na son ɗauko Gimenez
Valencia ta dage cewa ba za ta rage farashin Ferran Torres, mai shekara 21 ba, a yayin da Manchester City ke son dauko dan wasan na Sufaniya mai buga tamaula a rukunin 'yan kasa da shekara 21. (Telegraph - subscription required)
Chelsea tana sanya ido kan dan wasanAtletico Madrid da Uruguay Jose Gimenez, mai shekara 25, inda kocinta Frank Lampard yake son dauko shi don magance matsalar da ake samu a tsaron bayan kungiyar. (Telegraph - subscription required)
Lokacin da ake bikin kaddamar da shi a Bayern Munich, Leroy Sane, mai shekara 24, ya nuna alamar da ke tabbatar da cewa dan kasarsa ta Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, zai tafi Chelsea daga Bayer Leverkusen a bazarar nan. (Mail)
Chelsea da wakilin Havertz sun amince da yarjejeniya kan dan wasan tsakiyar na Leverkusen. (Nicolo Schira, via Star)
Brighton ba ta da niyyar sayar da dan wasan Ingila Ben White, mai shekara 22, ga Leeds United, inda ya yi zaman aro a kakar wasan bana. (Mail)
Bayern Munich ta ce ba za ta bar dan wasan Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29, ya bar kungiyar cikin rahusa ba, bayan da aka ce zai tafiLiverpool. (Metro)
Benfica ta daina zawarcin dan wasan Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 33, bayan da tsohon dan wasan na Paris St-Germain ya bukaci a rika biyansa £18m a duk kakar wasa daya. (A Bola - in Portuguese)
Kungiyar da ke buga gasar Serie C Como ta tabbatar cewa tana tattaunawa domin dauko tsohon dan wasan Manchester City da Liverpool Mario Balotelli. Dan wasan mai shekara 29 dan kasar Italiya ya sirya barin kungiyarsa Brescia. (La Provincia di Como, via Football Italia)
Mataimakin shugaban Manchester United Ed Woodward yana duba yiwuwar nada daraktan wasanni a kungiyar a bazarar nan. (Telegraph - subscription required)
Jesse Lingard, mai shekara 27, ya yi kira ga dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, ya bar Borussia Dortmund domin ya hadu da shi a Manchester United a bazarar nan. (Evening Standard)
Sancho yana cikin 'yan wasa biyar da kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer yake so ya kara domin hada tawagarsa. Sai dai watakila sai ya sayar da wasu 'yan wasansa domin samun kudin gudanar da wasu harkokin kungiyar. (Telegraph - subscription required).