Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Makomar Pochettino, Ake, Sancho, Gerrard, Havertz, Oblak da Ozil
Juventus na nazari kan ɗauko tsohon kocin Tottenham Mauricio Pochettino domin ya maye Maurizio Sarri a matsayin koci. (La Stampa, via Mail)
Manchester City na dab da kammala cinikin ɗan wasan baya na Bournemouth da Netherlands Nathan Ake, mai shekara 25. (Guardian)
Manchester United dole ta yanke shawara kan farashin fam miliyan £80 na ɗan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20. (Star)
KocinRangers Steven Gerrard Bristol Cityna harinsa domin zama sabon kocinta. (Bristol Post)
Chelsea na tattaunawa da Bayer Leverkusen kan farashin fam miliyan £70 game da Kai Havertz, inda sauran ƙungiyoyin da ke son ɗan wasan mai shekara 21 na Jamus ake tunanin sun janye. (Sky Sports)
Chelsea sai ta biya ɗan wasan Slovenia Jan Oblak yuro miliyan 120 kafin karɓo golan mai shekara 27 daga Atletico Madrid. (Goal)
Dan wasan tsakiya na ArsenalMesut Ozil, mai shekara 31, ya yi watsi da tayin ƙungiyar Turkiya Fenerbahce. (Bild)
Amma akwai yiyuwar Ozil zai koma taka leda gasar Super Lig a ƙungiyar Istanbul Basaksehir da ta lashe kofin gasar kuma ke harinsa. (90min)
West Ham ba ta da shirin buɗe tattaunawa kan sabunta kwangilar kaftin ɗinta Mark Noble, mai shekara 33, wanda yarjejeniyarsa za ta kawo ƙarshe a 2021. (Football Insider)
Bayan watsi da tayi biyu, Tottenham na da tabbaci kan ɗauko dan wasan Beijing Guoan da Koriya ta Kudu Kim Min-jae, wanda ake kwatantawa da Virgil van Dijk na Koriya. (90min)
Southampton na amince ta biya £10.9m kan dan wasan Ghana Mohammed Salisu, mai shekara 21, daga Real Valladolid bayan kammala yarjejeniya da ɗan wasan inda za ta dinga biyansa fam dubu 35,000 a shekara. (Football Insider)
Newcastle na sa ido kan ɗan wasan tsakiya na Motherwellda Scotland David Turnbull, mai shekara 21, wanda ake alakantawa da Celtic. (Newcastle Chronicle)
Burnley na son dan wasan tsakiya na Southampton Harrison Reed, mai shekara 25, wanda ya nuna bajinta a mtasayin ɗan wasan aro a Fulham. (Football Insider)
Kocin Brighton Graham Potter ya ce zai fi mayar da hankali wajen gida tawagarsa maimakon cefanen ƴan wasa. (Argus)
KocinWolves Nuno Espirito Santo ya amincewa cewa kullen korona ya yi tasiri akansa inda ya ce bai ga iyalinsa ba sama da wata biyu. (Express & Star)
Manchester United na fatan sanar da sayen matasan ƴan wasa Marc Jurado, mai shekara 16, da Alvaro Fernandez, mai shekara 17 da kuma ɗan wasan Norway na gaba Isak Hansen-Aaroen, mai shekara 15. (Manchester Evening News)