Ina son 'yan wasanmu su fito daga makarantar Liverpool - Klopp

Jurgen Klopp na fatan nan gaba 'yan wasan Liverpool za su kasance wadanda suka fito daga makarantar horar da 'yan kwallon kungiyar.

A ranar Asabar dan kwallon da ke buga tsakiya, Curtis Jones wanda aka haifa a Liverpool wanda ya fito daga karamar kungiyar ya sa hannu kan yarjejeniyar shekara biyar.

Jones din mai shekara 19, shi ne ya ci wa Liverpool kwallo na biyu da ta doke Aston Villa 2-0 ranar Lahadi, kuma na farko da ya ci a gasar Premier League.

Klopp ya ce ''Ina fatan kungiyarmu za ta kunshi 'yan wasan da suka karbi horo a makarantar koyar da tamula ta Liverpool''.

Wasu daga cikin fitattun 'yan kwallon da suka buga wa Liverpool daga karamar kungiyar sun hada da Steven Gerrard da kuma Jamie Carragher wadanda aka haifa a Merseyside.

Tuni Liverpool ta lasshe kofin Premier League na bana kuma karon farko tun bayan shekara 30.

Liverpool wacce aka fitar daga gasar Champions League da FA Cup na bana za ta ziyarci Brighton a wasan mako na 34 a gasar Premier League ranar Laraba.

Kungiyar ta hada maki 89 tana kuma fatan hada maki fiye da 100 a kakar tamaula ta shekarar nan, domin haura tarihin da Manchester City ta kafa.