Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tottenham ta ci Everton 1-0 inda Lloris da Son suka kusa dambatawa
Jose Mourinho ya ci wasa na 200 a gasar Premier League, bayan da Tottenham ta ci Everton 1-0 a karashen wasan mako na 33 ranar Litinin.
Sai dai kuma kadan ya rage a bai wa hammata iska tsakanin mai tsaron raga Hugo Lloris da Son Heung-min.
Kyaftin din Tottenham ne Lloris ya yi gudu ya je ya dafa bayan Son ya kuma ture shi.
Nan da nan dan kwallon tawagar Koriya ta Kudu ya juya cikin fushi zai kalubalanci golan Faransa sai wani abokin wasa ya shiga tsakani.
Sai dai bayan da aka tashi daga karawar 'yan wasan biyu sun mance da abinda ya faru har ma suka rungumi juna.
Tottenham ta ci kwallo ne bayan da dan wasan Eveton, Michael Keane ya ci kansu, kuma karo na uku Everton na cin kanta da kanta a bana.
Wannan ne karo na hudu a kakar shekarar nan da abokan karawa ke cin kansu a fafatawa da Everton a gasar Premier League.
Da wannan sakamakon Tottenham ta koma ta takwas da maki 48, ita kuwa Everton tana ta 11 da maki 44.
Tottenham za ta ziyarci Bournemouth a wasan mako na 34 ranar Alhamis, yayin da a dai ranar Everton za ta karbi bakuncin Southampton.