'A Barcelona Lionel Messi zai yi ritaya daga buga kwallon kafa'

Lionel Messi zai karkare sana'arsa ta kwallon kafa a Barcelona in ji shugaban kungiyar Maria Bartomeu.

Bartomeu, ya yi watsi da batun cewar kyaftin din tawagar Argentina, mai shekara 33 ba zai tsawaita zamansa a kungiyar da kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2021 ba.

Shugaban ya fada a wata hira da aka yi da shi a Movistar a Spaniya ''Muna tattaunawa da 'yan wasa da dama kan tsawaita zamansu a Barcelona,

Messi kuma ya sanar da mu cewar zai ci gaba da taka leda a Camp Nou, kuma muna murna da wannan matakin da ya yanke.''

Barcelona ta koma mataki na biyu a kan teburi tun da aka ci gaba da gasar La Liga ta bana, bayan ita ce kan gaba kan a dakatar da gasar cikin watan Maris saboda cutar korona.

Real Madrid ce yanzu ke kan teburi da tazarar maki hudu tsakaninta da Barcelona ta biyu.

Ita dai Real Madrid ta cinye dukkan wasanninta tun bayan da aka koma buga gasar La Liga, yayin da Barca ta yi canjaras a karawa biyu.

Ranar Lahadi Barcelona ta doke Villareal da ci 4-1, ita kuwa Real ta yi nasara a kan Athletic Bilbao da ci 1-0 a bugun fenariti.

Ana kuma ci gaba da caccakar Madrid sakamakon lashe wasa biyu da ta yi a bugun fenariti, bayan wanda ta yi nasara a kan Getafe ranar Alhamis.

Kyaftin Sergio Ramos ne ke cin bugun fenaririn kuma kawo yanzu yana da 22 da ya ci wa Real Madrid da tawagar Spaniya har da uku da ya zura a raga tun da aka ci gaba da La Liga ta bana.