Ramos ya kai Madrid daf da lashe La Liga na bana

Sergio Ramos ne ya ci kwallon da Real Madrid ta yi nasara a kan Athletic Bilbao da ci 1-0 ta kuma bai wa Barcelona tazarar maki bakwai.

Karo na biyu a jere da kyaftin din ke samar wa da Real Madrid maki ukun da take bukata a wasannin La Liga na bana.

Ramos ya ci kwallon a bugun fenariti kamar yadda ya yi a karawa da Getafe a ranar Alhamis da Real ta ci 1-0.

Dani Garcia na Atletic Bilbao ne ya yi wa Marcelo keta kuma na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci wato VAR ta tabbatar da laifin.

Kawo yanzu kyaftin din ya ci kwallo biyar a wasa bakwai da dukkansu Real Madrid ta yi nasara tun daga lokacin da aka ci gaba da wasannin shekarar nan.

A daren nan mai rike da kofin bara, Barcelona za ta ziyarci Villareal, kuma idan ta yi nasara tazarar da Real ta ba ta zai koma maki hudu kenan.

Kungiyar da Zinedine Zidane ke jan ragama na bukatar cin wasa uku daga hudun da suka rage a La Liga ta lashe kofin bana, wanda rabonta da shi tun 2016/17.