Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce zai kare kofin Premier a badi

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce za su ci gaba da salon kai hare-hare a wasannin kakar badi, maimakon tsare gida.

A makon jiya Liverpool ta lashe kofin Premier League na bana, kuma na farko tun bayan shekara 30, kuma saura wasa bakwai-bakwai a kammala wasannin bana.

Klopp wanda ya koma Liverpool a 2015 ya ce ''Za mu kare kofin da muka lashe za kuma mu ci gaba da salon kai hare-hare.

Liverpool ta bai wa Manchester City tazarar maki 23, wacce za ta fafata da ita ranar Alhamis a gasar Premier League.

Klopp ya ce ''A kakar badi Manchester United da Chelsea za su kara karfin kungiyoyinsu.''

''City za ta ci gaba da taka rawa a badi, United da Chelsea suna kan ganiya, musamman kungiyar Stamford Bridge na saka kwazo.''

Chelsea ce ta doke Manchester City 2-1 a Stamford Bridge da ya bai wa Liverpool damar lashe Premier League na bana saura wasa bakawi-bakawi a karkare kakar bana.