Man Utd za ta kara da Chelsea a wasan daf da karshe a FA Cup

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United za ta fafata da Chelsea, inda Arsenal za ta fuskanci mai rike da kofi Manchester City a wasan daf da karshe a FA Cup.
An raba jadawalin ne mai dauke da kungiyoyi uku da ke kan gaba a yawan lashe FA Cup har da Arsenal mai 13 jumulla.
United, wacce ta doke Norwich City ta kai wannan matakin tana da shi 12 jumulla, ita kuwa Chelsea da ta ci Leicester City tana da shi guda takwas.
Za a buga dukkan wasan daf da karshe a Wembley a karshen makon 18 da kuma 19 ga watan Yuli.
An tsayar da ranar 1 ga watan Agusta domin buga wasan karshe a Wembley.
An raba jadawalin ne a lokacin da aka yi hutu a wasan da Newcastle United ke karbar bakuncin mai rike da kofin Manchester City, kuma City ce ta yi nasara da ci 2-0.
Arsenal wacce take kan gaba a lashe FA Cup ta kai fafatawar daf da karshe a bana, bayan da ta ci Sheffield United 2-1, kuma Dani Ceballos ne ya ci mata na biyun a minti na 91.
Wasan daf da karshe tsakanin United da kuma Chelsea maimaicin karawar karshe kenan da suka yi a 2018, inda kungiyar Stamford Bridge ta lashe kofin.











