Chelsea ta kai daf da karshe a FA Cup, bayan da ta ci Leicester City

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea ta kai fafatawar daf da karshe a gasar FA Cup, bayan da ta ci Leicester City 1-0 a King Power a wasan da suka yi ranar Lahadi.
Sai da suka yi mnti 45 ba ci aka je hutu, bayan da aka koma zagaye na biyu Frank Lampard ya sa Ross Barkley wanda ya ci mata kwallon.
Lampard da Chelsea na taka rawar gani tun lokacin da aka ci gaba da buga gasar Premier, inda kungiyar Stamford Bridge ta doke Aston Villa da Manchester City.
Hakan ya sa Chelsea na matakin da za ta iya karkare kakar bana cikin 'yan hudun farko, yanzu kuma ta kai wasan daf da karshe a FA Cup.
Ita kuwa Leicester na fama da kaka ni kayi tun da aka ci gaba da wasannin Premier League na shekarar nan.
Kungiyar da Brendan Rodgers ke jan ragama ta yi canjaras a gidan Watford da a gidanta da Brighton yanzu kuma ta fice daga FA Cup na bana.
Ranar Laraba Leicester City za ta ziyarci Everton a wasan mako na 32 a gasar Premier League.
A dai Ranar West Ham United za ta karbi bakuncin Chelsea a dai wasannin na Premier League na shekarar nan da tuni Liverpool ta zama zakara.,










