Ceballos ya kai Arsenal wasan daf da karshe a FA Cup

Nicolas Pepe scores from the penalty spot

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Pepe ya ci wa Arsenal kwallo takwas a kakar bana kuma na farko a gasar FA Cup

Dani Ceballos ne ya ci wa Arsenal kwallo na biyu da ya kai kungiyar wasan daf da karshe a FA Cup, bayan doke Sheffield United 2-1 ranar Lahadi.

Gunners ce ta fara cin kwallo ta hannun Nicolas Pepe a bugun fenariti, bayan da Chris Basham ya yi wa Alexandre Lacazette keta a da'ira ta 18..

Daga baya ne mai masukin baki, Sheffield ta farke ta hannun McGoldrick saura minti uku a tashi daga karawar.

Bayan da alkalin wasa ya kara lokaci ne Arsenal ta ci kwallo na biyu ta hannun Ceballos wanda ke buga wa kungiyar wasannin aro.

Wannan nasarar za ta kara wa Gunners kwarin gwiwa a shirin da take na shiga 'yan hudun farko a gasar Premier League ko samun gurbin buga Europa League a badi.

Arsenal tana mataki na tara a kan teburin Premier League da maki 43, kuma Gunners din za ta karbi bakuncin Norwich City ranar 1 ga watan Yuli.