Juventus tana son ɗauko Aubameyang, Koulibaly zai koma Manchester City

Pierre-Emerick Aubameyang

Asalin hoton, Getty Images

Juventus ta bi sahun wasu kungiyoyi wajen zawarcin kyaftin din Arsenal da Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31. Da ma Barcelona da Inter Milan suna son dauko dan wasan. (Le10 Sport - in French)

Ana sa ran dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, zai koma Manchester City a bazarar nan bayan Liverpool ta mayar da hankalinta zuwa wani dan wasan. (Express)

Manchester United ce kungiya daya tilo da dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20 zai zabi komawa a bazara. Sai dai Dortmund ba za ta sallama shi ba a kan ƙasa da £118m. (Bild - in German)

Dan wasan Brazil Fred, mai shekara 27, yana son sabunta kwangilarsa a Manchester United. (Sun)

Everton, Tottenham da kumaWolves suna son dauko dan wasan Paris St-Germain da Brazil Thiago Silva. Rahotanni na cewa dan kwallon kafar mai shekara 35 yana son komawa Ingila. (Goal - in Portuguese)

Liverpool ta zama kungiyar da ta fi samun damar sayen Thiago Alcantara a kan £43m bayan dan wasan Spaniya mai shekara 29 ya fice daga tattaunawar da suek yi da Bayern Munich. (Bild - in German)

Arsenal ta tuntubi Sporting Lisbon game da yiwuwar dauko dan wasan Portugal Joelson Fernandes, dan shekara 17. Sai dai Barcelona da RB Leipzig suna zawarcin dan wasan. (O Jogo via Star)

Kocin Saint-Etienne Claude Puel yana so a tsawaita zama dan wasan Faransa mai shekara 21 William Saliba wanda ya karbo aro daga Arsenal har sai an kammala gasar Coupe de France. (Goal)

Dan wasan da Tottenhamta sayo a kan£54m Tanguy Ndombele, mai shekara 23, ya shaida wa kocin kungiyar Jose Mourinho cewa ba ya so ya kara buga tamaula a kungiyar. Paris St-Germain, Barcelona da Bayern Munich suna zawarcin dan wasan na Faransa. (ESPN)

Barcelona za ta so karbo Ndombele domin ta bayar da dan wasan Portugal Nelson Semedo, mai shekara 26, ko kuma dan wasan Brazil mai shekara 28 Philippe Coutinho - wanda yake zaman aro a Bayern Munich - ga Tottenham. (Independent)