Liverpool na son sayo Koulibaly, Chelsea za ta mayar da hankali kan Kurzawa

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea za ta iya mayar da hankalinta kan dan wasan Paris St-Germain dan kasar Faransa Layvin Kurzawa, mai shekara 27, idan suka gaza dauko dan wasan Leicester dan kasar Ingila Ben Chilwell, mai shekara 23. (Express)
Barcelona ta soma tattaunawa a kan sabunta kwangilar shekara biyu da dan wasan Argentina Lionel Messi, wanda zai shekara 33 ranar Laraba. (Marca)
Juventus ta shirya domin bai wa Wolves'yan wasan Italiya Daniele Rugani, mai shekara 25, da Federico Bernardeschi, mai shekara a yunkurin da take yi na rage tsadar sayen dan wasan Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29. (Tuttosport)
Liverpool na son sayo dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly a kan £54m. Manchester United da Chelsea ma suna zawarcin dan kwalln mai shekara 29. (Corriere dello Sport)
Roma ta yi tayin kwangilar shekara biyu ga dan wasan Tottenham dan kasar Belgium Jan Vertonghen, mai shekara 33, tare da ba shi zabin yin kakar wasa uku. (Il Messaggero, via Mail)
Everton tabi sahun wasu kungiyoyi da ke son dauko dan wasan Real Valladolid Mohammed Salisu, 21. Southampton da Manchester United suna don dauko dan kasar ta Ghana, wanda za a sayar a kan £10.8m (Mail)
Dan wasanEverton da Faransa Morgan Schneiderlin, mai shekara 30, yana shirin barin Goodison Park bayan an yi nasarar gwada lafiyarsa a Nice. (Sky Sports)
PFC Slavia Sofia ta ce ta cimma yarjejeniya da Manchester City domin kammala sayen dan wasan Bulgaria Filip Krastev, dan shekara18. (Manchester Evening News)
Wasu jami'an Birmingham City sun tashi daga kan kujerunsu domin kyale mahaifiyar Jude Bellingham ta zauna ta kalli fafatawar da suka yi da West Brom a gasar Zakarun Turai. Manchester United da Borussia Dortmund suna zawarcin dan wasan tsakiyar dan shekara 16 .(Mail)











