Makomar Cavani, Meunier, Bailey, Jorginho, Jimenez, Drinkwater da Ceballos

Asalin hoton, Getty Images
Juventus ta bi sahun Manchester United da Real Madrid da ke bukatar dan wasan gaba na Wolves da Mexico Raul Jimenez, mai shekara 29. (Calcio Mercato, via Mail on Sunday)
Dan wasan gaba na Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 33, da kuma dan wasan baya na Belgium Thomas Meunier, mai shekara 28, ba za su tsawaita kwantaraginsu ba da Paris St-Germain zuwa 30 Yuni wanda ke nufin ba za su buga wa kulub din gasar cin kofin zakarun Turai ba da za a fara watan Agusta. (RMC, via Mail on Sunday)
Chelsea, Manchester City da Manchester United na ribibin dan wasan Bayer Leverkusen Leon Bailey, mai shekara 22 wanda darajarsa ta kai fam miliyan 40. (Mail on Sunday)
Chelsea ta yi watsi da tayin Juventus na musayar Jorginho, mai shekara 28, domin karbo dan wasan Bosnia-Herzegovina Miralem Pjanic, mai shekara 30, daga Juventus. (Calcio Mercato, via Sunday Express)(Calcio Mercato, via Mail on Sunday)
Dan wasan tsakiya na Spain Dani Ceballos, mai shekara 23, zai ci gaba da zama a matsayin dan wasan aro a Arsenal daga Real Madrid har zuwa karshen kaka amma ya yadda zai ci gaba da zama dan wasan Real Madrid idan Zinedine Zidane ya ci gaba da horar da kulub din a Bernabeu zuwa badi. (Marca)
Arsenal ta amince da yarjejeniyar da ta kai ta fam miliyan £14m kan dan wasa Pablo Mari da ta karbo aro daga Flamengo . (Mail on Sunday)
Everton da Newcastle United na bukatar dan wasan AC Milan da Ivory Coast Franck Kessie, mai shekara 23. (Tuttosport, via Football Italia)
KocinAston Villa Dean Smith ya ce kulub din zai tsawaita kwantaragin golan Sifaniya Pepe Reina, mai shekara 37 wanda aka dauko daga AC Milan. (Birmingham Mail)










