Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Neymar: Abin da ya sa kotu ta ce dole dan wasan PSG ya biya Barcelona euro 6.7m
Wata kotun Spaniya ta ce dole dan wasan gaba na Paris St-Germain Neymar ya biya tsohuwar kungiyarsa Barcelona euro 6.7m.
Dan wasan Brazil ya yi ikirarin cewa yana bin Barca bashin euro 43.6m, kafin ya bar ta a watan Agustan 2017.
Alkalin ya bai wa kungiyar nasara a kan Neymar mai shekara 28, wanda ya shigar da kara kotu jim kadan bayan ya bar Barcelona, ko da yake zai iya daukaka kara.
Barcelona ta ce ta yi "maraba da hukuncin" kuma "za ta ci gaba da kare hakkokinta".
Neymar ya kuma mika korafi ga hukumar kwallon kafar duniya, Fifa, bayan Barca ta ki biyansa sakamakon barinta da ya yi zuwa PSG a 2017 a kan euro 222m.
Duk da rashin biyan dan wasan, Barcelona ta gurfanar da Neymar a kotu inda take so ya biya ta £8m wanda ya karba bayan ya sanya hannu a sabon kwantaragi da ita a 2016.
Fifa ba ta dauki wani mataki ba, tana mai cewa ta bar batun ga kotuna.