Dalilin da Mertens bai koma Chelsea da taka leda ba

Kadan ya rage Dries Mertens ya koma Chelsea da taka leda, yanzu zai tsawaita yarjejeniyar ci gaba da zama a Napoli in ji dan jarida Kristof Terreur.

Dan jaridar dan kasar Belgium ya ce tun cikin watan Janairu Chelsea ta kwankwasa kofa, ya kuma ce ''Da zarar kana taka leda a Kudancin Italiya kana karbar kudi mai tsoka kuma fitatce ne kai zai yi wuya ka sauya sheka''.

Terreur ya ce da ya amince zuwa buga gasar Premier ''Zai koma Chelsea ne a matsayin bako babu wanda ya san kwazonsa, yayin da yake tauraro a Italiya''.

Mertens, mai shekara 33 ya zama kan gaba a ci wa Napoli kwallaye a tarihi, inda ya ci ta 122 ranar Asabar a gasar Copa Italiya daa Inter Milan.

Hakan ne ya sa ya doke tarihin cin kwallaye da yawa da Marek Mamsik ya yi a kungiyar Napoli.

Kwantiragin dan kwallon tawagar Belgium zai kare a kakar bana, sai dai yana shirin sa hannu kan yarjejeniyar shekara uku duk da cewar Inter Milan da Chelsea na son zawarcin dan wasan.

Chelsea ta sayi dan kwallon Ajax, Hakim Ziyeck sannan Timo Werner na RB Leipzig ya amince zai koma Stamford Bridge da taka leda.