Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Timo Werner: Chelsea ta ƙulla yarjejeniyar ɗauko ɗan wasan RB Leipzig
- Marubuci, Daga Alistair Magowan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
Chelsea ta kulla yarjejeniya domin dauko dan wasan RB Leipzig Timo Werner.
Rahotanni sun ce za a sayar da dan wasan mai shekara 24, wanda ya ci kwallo 25 a gasar Bundesliga a kakar wasan da muke ciki, a kan £54m.
Ana ta rade radin cewa dan wasan dan kasar Jamus zai koma Liverpool ya kuma ce yana alfahari da jin dadin alakanta shi da batun.
Amma BBC Sport ta fahimci cewa Liverpool ba ta sha'awar sayen Werner, wanda ya ci wa tawagar Jamus kwallo 11 a wasa 29 da ya yi.
Liverpool ba ta da niyyar sayo dan wasa ko daya idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo.
Olivier Giroud ne kadai mai ci wa Chelsea kwallo da ke da lafiya, bayan da Tammy Abraham ke jinya tun cikin watan Janairu.
A watan jiya ne dan kwallon tawagar Faransa, Giroud ya sanya hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a Chelsea zuwa kakar wasa daya.
Werner zai kasance dan wasa na biyu da Chelsea za ta saya don buga wasa a kaka mai zuwa bayan kammala sayen dan wasan Ajax Hakim Ziyech a watan Fabrairu a kan £37m.
Ya burge Leipzig bayan komawa kungiyar a shekarar 2016 daga Stuttgart.
Werner ya ci kwallo uku a wasan da Leipzig ta doke Mainz da ci 5-0.
A watan Janairun an alakanta kocin Chelsea, Frank Lampard da cewar zai sayo dan wasan Paris St-Germain, Edinson Cavani da kuma na Napoli, Dries Mertens, ko da yake hakan zai yiwu ba.