Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Timo Werner: Chelsea na shirin sayen dan kwallon RB Leipzig
Chelsea na tattaunawa da RB Leipzig kan a sayar mata da Timo Werner.
Ana ta alakanta dan wasan mai shekara 24 dan kasar Jamus da cewar zai koma Liverpool ya kuma ce yana alfahari da jin dadin wannan batun.
Werner ya ci kwallo 25 a gasar Bundesliga a kakar nan ya kuma ci wa tawagar Jamus kwallo 11 a wasa 29 da ya yi.
Olivier Giroud ne kadai mai ci wa Chelsea kwallo da ke da lafiya, bayan da Tammy Abraham ke jinya tun cikin watan Janairu.
A watan jiya ne dan kwallon tawagar Faransa, Giroud ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a Chelsea zuwa kaka daya.
A cikin watan Janairun an alakanta kocin Chelsea, Frank Lampard da cewar zai sayo dan wasan Paris St-Germain, Edinson Cavani da kuma na Napoli, Dries Mertens.
A cikin watan Fabrairu Chelsea da dauko dan wasan Ajax, Hakim Ziyech kan fam miliyan 37.