Muna bukatar mai cin kwallaye — Lampard

Kocin Chelsea, Frank Lampard ya bayyana gurbin mai cin kwallo ne suke da matasala dalilin da suka kasa doke Newcastle ranar Asabar.

Newacastle United ta yi nasara a kan Chelsea da ci 1-0 a St James Park, karawar mako na 23 a gasar Premier.

A fafatawar Chelsea ta samu damarmaki 19, amma guda hudu ne suka nufi raga kai tsaye.

Lampard ya ce ''Idan har muna neman 'yan wasan da zamu dauka to gurbin masu cin kwallo muke bukata''

Ya kara da cewar ''Hakika kowa yasan matsalar da muke fuskanta, kuma wannan gurbin ya kamata mu karfafa.''

Lampard ya ce idan har baka cin kwallo a lokutan wasanni to kuwa a Premier za a iya baka mamaki.

Chelsea ta ci gaba da zama ta hudu a kan teburin Premier da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester United wadda za ta kara da Liverpool ranar Lahadi.