Sancho ba zai koma Liverpool ba, Werner ba shi da makoma a RB Leipzig

Jadon Sancho

Asalin hoton, Getty Images

Manajan tawagar Borussia Dortmund Sebastian Kehl ya yi watsi da rade radin da ake yi cewa Jadon Sancho zai koma Liverpool a bazarar nan. Ita ma Manchester United tana sha'awar dauko dan wasan na Ingila mai shekara 20. (Mirror)

Kocin RB Leipzig Julian Nagelsmann ya ce Timo Werner ba shi da makoma a kungiyar a yayin da dan wasan mai shekara 24 dan kasar Jamus yake jiran kammala komawa Chelsea. (Mirror)

Sai Kepa Arrizabalaga ya buga wasa tara nan gaba idan yana so ya nuna cewa yana da kwazo a Chelsea, a yayin da ake cewa akwai manyan 'yan wasan da za su maye gurbin golan mai shekara 25. (Express)

Da alamaArsenal za ta yi nasarar dauko dan wasan Faransa Dayot Upamecano, a yayin da Manchester United da Bayern Munich suke son dauko dan wasan na RB Leipzig mai shekara 21. (Tuttosport - in Italian)

Jorginho da kocin Juventus Maurizio Sarri basu yi magana ba tun da manajan ya bar Chelsea, amma ana ci gaba da alakanta dan wasan mai shekara 28 da yiwuwar komawa kungiyar da ke buga Gasar Serie A. (Daily Mail)

Dan wasan Celtic Odsonne Edouard ya yi watsi da rade radin da ake yi cewa zai koma Arsenal, inda dan wasan mai shekara 22 ya ce yana son zama daya daga cikin nasara ta 10 ta lashe kofi da kungiyar ta Scotland za ta yi. (Daily Mail)

Juventus tana da kwarin gwiwar sabunta kwangilar dan wasan gaba na Argentina Paulo Dybala, a yayin da dan wasan mai shekara 26 yake so a biya shi £11m duk shekara. (Goal)

KocinMainz Rouven Schroder ya ce kungiyarsa tana tattaunawa domin rike dan wasan gaba na Liverpool Taiwo Awoniyi. Dan wasan na Najeriya mai shekara 22 yana zaman aro a kungiyar tun bazarar da ta wuce. (Goal)

Dan wasan Chile Arturo Vidal, mai shekara 33, ya nuna sha'awarsa ta komawa Inter Milan, yana mai cewa ba a daukarsa da muhimmanci a Barcelona. (Goal)

Edinson Cavani, mai shekara 33, zai bar Paris St-Germain tare da Thiago Silva, mai shekara 35, a karshen watan Agusta, a cewar daraktan wasannin kungiyar. (Le Journal du Dimanche - in French and subscription only)