Borussia Dortmund za ta sayar da Sancho a kan £115m, PSG tana zawarcin Wilfried Zaha

Jadon Sancho

Asalin hoton, EPA

Borussia Dortmund za ta sayar da dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho a kan £115m. (Telegraph)

Paris St-Germain tana son dauko dan wasan Ivory Coast mai shekara 27, Wilfried Zaha. (90 Min)

Southampton tana shirin sabunta kwangilar dan wasan Ingila Ryan Bertrand, mai shekara 30, a yayin da Leicestertake zawarcin dan wasan.(Daily Mail)

Golan PolandBournemouth Artur Boruc, mai shekara 40, dan dan wasan tsakiya na Ingila Andrew Surman, mai shekara 33, da takwarorinsa masu tsaron baya Simon Francis, mai shekara 35, da Charlie Daniels, mai shekara 33, na shirin sanya hannu kan kwangilar gajeren lokaci. (Bournemouth Echo)

Dan wasan tsakiya na Scotland Ryan Fraser, mai shekara 26, yana shirin yin watsi da tayin da Bournemouth za ta yi masa na kwangilar gajeren lokaci, kuma hakan na nufin zai iya barin kungiyar a bazara. (Sun)

Damar da Chris Hughton zai samu ta sake zaman kocin Birmingham ba ta da yawa. (Birmingham Mail)

Manchester United za ta fafata daWest Brom a wasanni biyu a Old Trafford ranar Juma'a, a yayin da suke shirin komawa Gasar Premier. (Telegraph)

Dan wasan SpaniyaVillarreal Santi Cazorla, mai shekara 35, ya ce ya yanke hukunci kan makomarsa - amma bai bayyana inda zai koma ba. Kwangilar tsohon dan wasan na Arsenal za ta kare a bazarar da muke ciki. (Cadena Ser via Mirror)

Leicester City tana shirin zama kungiyar Gasar Premier ta baya bayan nan da za ta sanya karin kudin masu yawa a kan tawagar kwallon kafar mata da zummar karfafa Gasar Zakaru - gasa ta biyu mafi girma ta mata 'yan kwallon kafa. (Times - subscription required)

Shugabannin Real Madrid cikin girmamawa sun ki amincewa da tayin da aka yi musu na buga wasanninsu shida na karshe na gida a Wanda Metropolitano - filin wasan da ke gogayya da Atletico Madrid. A halin da ake cikiana yin gyare-gyare a filin wasan Real, wato Santiago Bernabeu. (Marca)