Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Suarez zai buga wa Barcelona wasa bayan kwana 147 yana jinya
Luis Suarez ya murmure zai kuma ci gaba da buga wa Barcelona sauran wasannin La Liga da suka rage a bana, bayan kwana 147 da likitoci suka yi masa aiki.
Ana kuma sa ran dan kwallon zai buga wa Barcelona wasan da za ta fafata da Real Marca ranar 13 ga watan yuni da za a ci gaba da wasannin 2019-20.
Ranar 12 ga watan Janairu aka yi wa likitoci suka yi wa Suarez aiki, inda suka gindaya masa karshen kakar bana zai murmure.
Wasan karshe da ya buga wa Barcelona shi ne karawa da Atletico Madrid a farkon makon Janairu a wasan daf da karshe a Spanish Super Cup.
Suarez ya koma atisaye a cikin watan Mayu, bayan wata hudu rabonsa da taka leda, kawo yanzu ya koma kan ganiyarsa zai iya buga wa Barca sauran wasannin La Liga da suka rage a bana.
Dan wasan na tawagar Uruguay ya ci kwallo 14 a wasa 23 da ya buga wa Barcelona a kakar shekarar nan, guda 11 a La Liga da uku da ya ci a Champions League.
Duk da jinya da Suarez ya yi shi ne ke mataki na uku a jerin wadanda suka bayar da kwallo aka zura a raga a gasar ta La Liga, inda yake da takwas.
Tun cikin watan Maris aka dakatar da wasannin La Liga don gudun yada cutar korona, bayan da Barcelona ce ta daya a kan teburi da tazarar maki biyu tsakaninta da Real Madrid.