La Liga: Za a yi wa Suarez tiyata a gwiwarsa

Za a yi wa dan wasan gaban Barcelona Luis Suarez tiyata a kokon gwiwarsa ranar Lahadi.

Dan wasan kasar Uruguay din mai shekara 32 ya ji rauni a gwiwarsa ta dama kuma kwararren likitan kasar Sifaniya ne wato Dakta Ramon Cugat zai yi masa aikin.

Suarez ya buga baki dayan wasan da Barcelona ta kara da Atletico Madrid ranar Alhamis, wanda Atletico din ta casa su da ci 3-2 a wasan kusa da na karshe na gasar Spanish Super Cup.

Dan wasan ya buga wa Barca wasa 23 a kakar bana, inda ya ci kwallo 14.