Spain Super Cup: Atletico Madrid ta doke Barcelona

Angel Correa ya taimakawa Atletico Madrid doke Barcelona 3-2 a Saudiyya a gasar lashe Super Cup.

Koke ya fara zira wa Atletico kwallo a raga bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Lionel Messi ya farke kwallon kafin Antoine Griezmann ya sake jefa wa Barcelona kwallo ta biyu.

Alvaro Morata kuma ya farke wa Atletico a bugun fanariti kafin dab da hure wasa Correra ya jefa kwallo ta uku a ragar Barcelona.

Akwai dai kwallon da Messi ya ci amma na'urar tantance kwallo a raga ta soke saboda kwallon ta tabi hannunsa.

Nasarar da Atletico Madrid ta samu na nufin za ta hadu da makwabciyarta Real, wacce ta doke Valencia 3-1 ranar Laraba, a wasan karshe da za su fafata ranar Lahadi.

An sauya tsarin gasar a bana zuwa kungiyoyi hudu maimakon biyu inda kungiyoyi biyu da suka jagoranci La Liga da kuma wadanda suka buga wasan karshe a Copa del Rey za su dinga buga super Cup.

Real Madrid ce ta kare a matsayi na uku La Liga a kakar da ta gabata, amma ta shiga gasar ne saboda Barcelona ta lashe La liga tare da zuwa na biyu a Copa del Ray.