Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Atletico Madrid: Ba na shakkar kowane kulob – Diego Simeone
Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya ce "idan 'yan wasana na kan ganiyarsu ba na shakkar kowa" yayin da yake shirn gwabzawa da Real Madrid a wasan karshe na Spanish Super Cup.
Za a buga wasan ranar Lahadi a filin wasa na King Abdullah Sports City na kasar Saudiyya bayan Atletico ta lallasa Barcelona ranar Alhamis .
"Karawa da kungiyoyi irin su Real Madrid da Barcelona da Liverpool na kara mana kwarewa," Simeone ya bayyana a wurin taron manema labarai gabanin wasan.
Ya ci gaba da cewa: "Irin wadannan wasanni ba irin wadanda muka saba bugawa a Laliga ba ne.
"Ina da kwarin gwiwa a kan 'yan wasana kuma za mu karfafa kungiyar. Duk sanda suke kan ganiyarsu ba na shakkar kowace kungiya.
"Ban san me zai faru ba idan muka samu nasara. Dole ne mu buga wasan da azama. A wurinmu babu wani abu mai muhimmanci sama da wasan gobe (Lahadi) kuma dama ce mai kyau a gare mu."
Mai tsaron raga Oblak da kuma Ángel Correa sun ji rauni, "amma za mu duba mu ga yadda za su yi atasaye a yammacin yau sai mu ga yadda za a yi," in ji Simeone.