Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Alexander-Arnold da Klopp su ne gwarazan Premier
Dan wasan Liverpool, Trent Alexander-Arnold ya zama dan wasan kwallon kafa da ya fi kowanne a gasar Premier Ingila a watan Disamban 2019.
Shi kuma kocin kulob din, Jurgen Klopp ya lashe kyautar kocin da ya yi fice a gasar, inda kuma ya samu matsayin karo hudu a kakar wasa ta bana.
Alexander-Arnold, mai shekara 21 dai ya zura kwallo guda ya kuma taimaka a ci guda uku sannan shi ne taimaka wa kulob din nasa samun nasara har sau uku al'amarin da ya ba shi nasarar samun kyautar a karo na farko.
Kulob din Liverpool dai wanda shi ne a saman teburin gasar ta Premier ya yi nasara a dukkanin wasanninsa guda biyar da ya taka a watan Disamba.
Shi kuwa Jurgen Klopp, mai shekaru 52, ya samu abin da ya daidaita kwazonsa da na Pep Guardiola a kakar wasa.
Pep Guradiola ya ci wasannin hudu a kakar wasa ta 2018-2019, inda kulob din nasa na Manchester City ya lashe gasar da maki 100.
Liverpool ta bai wa mai biye mata a baya tazarar maki 13 bayan taka wasanni guda 20 ba tare da yin nasara a kanta ba.