Suarez din Barcelona zai yi jinya mai tsawo

Dan wasan Barcelona, Luis Suarez zai yi jinya zuwa wata hudu, bayan raunin da ya yi a gwiwar kafarsa.

Tuni wani kwararren likitan Spaniya, Dakta Ramon Cugar ya yi wa Suarez aiki.

Suarez ya buga wa Barcelona karawar da Atletico Madrid ta yi nasara da ci 3-2 a wasan Spanish Super Cup da suka kara a Saudi Arabia.

Dan wasan mai shekara 32, ya ci kwallo 14 a wasa 23 da ya buga wa Barcelona a kakar bana.

Barcelona mai rike da kofin La Liga tana ta daya a teburin bana, mai maki iri daya da na Real Madrid.

Real Madrid tana buga wasan karshe da Atletico Madrid ranar Lahadi a gasar Spanish Super Cup.

Real ta kai wasan karshe ne, bayan da ta doke Valencia da ci 3-1.