Real Madrid ta bayar da euro 80m don sayo Havertz, Everton za ta ɗauko Rabiot

Real Madrid ta mika euro 80m domin sayo dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz kuma za ta kyale dan wasan na Jamus mai shekara 20 ya ci gaba da zama a kungiyarsa ta yanzu zuwa kakar wasa ta baɗi kafin ya koma Bernabeu. (ESPN via Bild)

Chelsea za ta yi maraba da kungiyoyin da ke son daukar 'yan wasanta da dama bayan isar dan wasan Morocco Hakim Ziyech, mai shekara 27, daga Ajax da kuma dan wasan Jamus Timo Werner, mai shekara 24, dagaRB Leipzig a bazarar nan. (Daily Star on Sunday)

Shugaban Red Bull Leipzig Oliver Mintzlaff ya musanta cewa Chelsea ta cika sharudan biyan £53m a kan Werner, yana mai cewa babu kungiyar da ta "aiko mana da kwangilar musayar 'yan kwallo". (Sky Sports Germany via Metro)

KocinLiverpool Jurgen Klopp ya bayyana Havertz da Werner a matsayin "manyan" 'yan wasa amma ya ce matsalolin da annobar korona ta kawo za su iya shafar shirinsa na dauko su. (Sky Sports)

Everton tana kan gaba a fafutukar dauko dan wasan Juventus da Faransa mai shekara 25 Adrien Rabiot, wanda a 2012 kocin Everton Carlo Ancelotti ya soma sanya shi a wasa a tsohuwar kungiyarsa Paris St-Germain. (Tuttosport via Mail on Sunday)

Chelsea tana fuskantar kalubale daga kungiyoyi akalla bakwai a yunkurin da take yi na dauko dan wasan Ingila Ben Chilwell daga Leicester, wadda ake matsawa lamba domin ta sayar da dan wasan mai shekara 23. (Sunday Mirror)

Arsenal da Wolves suna sha'awar dauko dan wasan Italiya mai shekara 25 Daniele Rugani, wanda ya yi ta fama wajen ganin an sanya shi a tawagar farko a Juventus lokacin jagorancin Maurizio Sarri.(Tuttosport via Mail on Sunday)

Manajan Netherlands Ronald Koeman ya ki amsa tayin komawa Barcelona a watan Janairu saboda ba ya so ya ci amanar tawagar kasar Netherlands. (AS)