Bayern Munich na bukatar cin wasa biyu a ba ta Bundesliga na bana

Bayern Munich na bukatar cin wasa biyu nan gaba daga hudun da suka rage a ba ta kofin Bundesliga na takwas a jere bayan da ta doke Bayer Leverkusen ranar Asabar.

Bayern ta ziyarci Leverkusen ne a wasan mako na 30 a gasar Bundesliga, karawa ta hudu tun lokacin da aka ci gaba da gasar, bayan da cutar korona ta dakatar da wasanni a watan Maris.

Kungiyar da Hans Flick ke jan ragama ta yi rashin nasara a wasa daya tal daga 21 a baya a dukkan fafatawa a bana, Leverkusen ce ta fara cin kwallo daga baya ta farke ta kara uku.

Wadanda suka ci wa Bayern kwallayen sun hada Kingsley Coman da Leon Goretzka da kuma Serge Gnabry tun kan hutu, bayan da Lucas Alario ya fara ci wa Leverkusen.

Daga baya ne Robert Lewandowski ya ci kwallo kuma na 30 da ya zura a raga a kakar bana shi ne kan gaba a gasar.

Bayern ta yi rashin nasara a wasa biyu daga 26 da ta buga tun lokacin da Flick ya maye gurbin Niko Kovac wanda aka kora a cikin watan Nuwamba.

A kuma ranar Laraba Bayern za ta buga wasan daf da karshe a kofin kalubalen Jamus da Eintracht Frankfurt ranar Laraba.