A karon farko an sauya 'yan wasa biyar a tarihin Bundesliga

Ranar Asabar aka ci gaba da wasannin gasar Bundesliga karawar mako na 26 ba tare da 'yan kallo ba.

Hukumar gudanar da gasar Jamus ta yi hakan ne don kaucewa yada cutar korona, inda ta dauki matakai da dama, bayan gwajin 'yan kwallo.

An fara ne da wasa shida a ranar ta Asabar, kuma karawar da ta ja hankalin masu bin harkokin kwallon kafa ita ce tsakanin Borussia Dortmund da Shalke 04.

Dortmund ce ta yi nasara da ci 4-0, kuma tun kan a buga wasan Borussia Dortmund tana da maki 51, ita kuwa Schalke tana da 37.

A fafatawar ce a karon farko a tarihin Bundesliga, Schalke ta sauya 'yan wasa biyar a tsarin da aka amince da shi don ragewa 'yan kwallo gajiya ganin za su yi wasa da yawa kuma daf da daf.

Shalke ta fara canji ana komawa zagaye na biyu, inda Burgstallerat ya canji Todibo, sannan Matondoat ya maye gurbin Raman.

A minti na 74 ana taka leda ne Shalke ta yi canji na uku inda Schöpfat ya canji Serdar, kuma minti biyu tsakani Mirandaat ya maye gurbin Caligiuri.

Schalke ta yi canji na karshe kuma na biyar saura minti uku a tashi daga wasan inda Beckerat ya canji Kenny.

Hakan ne ya sa kungiyar ta zama ta farko da ta amfana da wannan dokar da kwamitin shugabannin kwallon nahiyoyi na Fifa ya amince da shi.

Hakla kuma gasar ta zama ta farko da ta fara amfani da canjin 'yan wasa shida da aka amince za a dinga yi zuwa karshen watan Disamba don ragewa 'yan kwallo gajiya.

Haka kuma gasar ta Bundesliga ta zama ta farko da aka ci gaba da karawa a Turai, tun bayan da aka dakatar da ita cikin watan Maris don gudun yada cutar korona.