Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man Utd na son ɗauko Kai Havertz, Leicester 'bata damu da yunƙurin ɗauke Chilwell ba'
Manchester United ta mayar da hankali wajen dauko kyaftin din Aston Villa Jack Grealish, mai shekara 24, a bazarar nan - amma za ta iya sauya ra'ayi idan dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz zai amince ta dauko shi. (Manchester Evening News)
Sai dai a gefe daya, Bayern Munich ta yi amannar cewa tana dab da doke United - da ma wasu kungiyoyin kwallon kafar Turai - a fafutukar dauko Havertz mai shekara 20. (Independent)
Leicester City ta ce hankalinta a "kwance yake" duk a yunkurin daChelsea take yi na dauko dan wasanta mai shekara 23 Ben Chilwell, tana mai amannar cewar dan wasan zai ci gaba da zama tare da su idan suka samu gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai na baɗi. (Leicester Mercury)
Kazalika an ce Leicester City za ta nemi a biya ta akalla £60m a kan Chilwell. (Guardian)
Dan wasanManchester City Leroy Sane zai sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar a Bayern Munich. Amma dan kasar ta Jamus mai shekara 24 ba zai zama dan wasa mafi tsada a gasar Jamus ba. (Bild)
Everton ta shirya tsaf domin zawarcin kyaftin din Paris St-Germain Thiago Silva, wanda kwangilarsa za ta kare a karshen watan Yuni. AC Milan, wato tsohuwar kungiyar dan wasan mai shekara 35 dan kasar Brazil, tana son sake dauko shi. (Le10Sport)
Arsenal tana sha'awar dauko dan wasan Norwich City Max Aarons, mai shekara 20, ko da yake ta ce ba za ta iya biyan £30m a kansa ba. (Goal via Norwich Evening News)
Manchester City ta nemi dauko dan wasan Barcelona Sergi Roberto. Amma dan wasan na Spaniya mai shekara 28 ba zai iya barin Nou Camp ba sai kungiyar ta amice ya tafi. (Mundo Deportivo, in Spanish)
Ƙarshenta dan wasanNewcastle United Matty Longstaff, mai shekara 20, zai koma Watford idan ya sanya hannu a yarjejeniya da kungiyar Udinese, ganin cewa kungiyoyin biyu mallakin iyalan Pozzo ne. (Watford Observer)
Inter Milan ta ce za ta duba yiwuwar sayar da dan wasan Slovakia Milan Skriniar, wanda ake cewa zai koma Manchester City ne kawai idan aka biya ta €80m a kansa. (Tuttosport via Manchester Evening News)
Manchester United ta soma tattaunawa da kungiyar Argentina Velez Sarsfield da zummar dauko dan wasanta dan shekara 19 Thiago Almada, wanda za a sayar a kan £20m kuma ake rade radin zai koma Arsenal. (Fichajes, in Spanish)
Aston Villa da West Bromwich Albion za su fafata a wasan atisaye a wani bangare na shirin sake ci gaba da kakar wasa ta bana. (Daily Mail)