Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Chilwell yana son komawa Chelsea, Liverpool ta janye daga batun ɗauko Werner
Dan wasan Ingila Ben Chilwell, mai shekara 23, yana son amsa tayin da aka yi masa na komawa Chelsea nan gaba a bazara ko da yake har yanzu ba a gaya masa ya bar Leicester City ba. (Mirror)
Liverpool ba za ta yi gogayya da Chelsea a fafutukar dauko Timo Werner mai shekara 24 ba domin kuwa dan wasan na RB Leipzig da Jamus yana dab da komawa Stamford Bridge. (Evening Standard)
Tottenham tana jiran dan wasan Belgium Jan Vertonghen, mai shekara 33, ya yanke shawara kan ko zai kammala kakar wasa ta bana ko kuma zai bar kungiyar kafin a gama kakar. (Sky Sports)
Dan wasan Newcastle Matty Longstaff bai yi atisaye ba a wannan makon saboda fargabar rashin sanin makomarsa a kungiyar, a yayin da rahotanni suke cewa Udinese tana son dauko dan wasan inda za ta rika ba shi £30,000 duk mako. A bazarar nan kwangilar dan wasan za ta kare a Newcastle. (Mail)
Manchester City za ta soma tattaunawa don sabunta kwangilar dan wasan Spaniya dan shekara 19 Eric Garcia a yayin da tsohuwar kungiyarsa Barcelona take zawarcin dan wasan.(Mail)
Manchester United ta shirya domin bai wa dan wasan Ingila mai shekara 19 Brandon Williams, babbar kwangila, inda za ta inganta kudin da ake ba shi daga £4,000 da yake karba duk mako, bayan ya taka rawar gani a kakar wasan bana. (Athletic - subscription required)
WatakilaLiverpool za ta iya daukar Kofin Gasar Premier ta bana da misalin karfe 9 na dare a agogon Najeriya da Nijar ranar Lahadi a wasansu da Everton domin za a mayar da wasanninsu biyu maraice. (Mail)
Mai yiwuwaArsenal za ta sayar da dan wasa Scotland Kieran Tierney, mai shekara 23, ga Leicester City, wata 12 bayan ya koma Emirates. (Express)