Jurgen Klopp na kewar wasannin kwallon kafa

Jurgen Klopp celebrating with Roberto Firmino

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Klopp ya lashe wasa 27 daga 29 da ya ja ragamar Premier League a kakar 2019-20

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya shaida wa BBC cewar yana kewar wasan kwallon kafa ya kuma yi murna da za a ci gaba da gasar Premier League ta bana.

Ranar 17 ga watan Yuni ake sa ran ci gaba da wasannin Premier League da kwantan wasa tsakanin Aston Villa da Sheffield United da na Manchester City da Arsenal.

Sauran wasannin za a ci gaba da buga su a karshen mako ne daga 19 zuwa 21 ga watan Yuni.

Liverpool ce ta daya a teburin shekarar nan da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City, kuma karon farko da ta lashe kofin tun bayan shekara 30.

Ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da gasar Premier saboda bullar cutar korona, kuma wasan karshe da aka yi shi ne wanda Leicester City ta doke Aston Villa 4-0 ranar 9 ga watan Maris.

Klopp ya fada wa BBC cewar ''Ina kewar wasannin kwallon kafa''

ya kara da cewar ''Na san ba ita kadai ce mafi mahimmaci a rayuwa, amma abinda nake kauna kenan. Ina fatan mutane ma sun kagu a ci gaba da wasanni''.

Liverpool za ta iya lashe kofin bana idan har Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Arsenal a wasan da za su kara 17 ga watan nan.

Saura karawa 92 a karkare gasar Premier League ta 2019-20.

Ranar Labara kungiyoyin Premier suka amince da yin atisaye na bai daya tare da hada jiki, bayan da aka yi na 'yan wasa cikin rukuni ba tare da gogayya da juna ba.

An samu mutun 12 dauke da cutar korna da ke hulda da gasar Premier, bayan gwajin mutum 2,752 da aka yi.

Za kuma a ci gaba da gwajin 'yan wasa da jami'ai a duk mako biyu daga mutum 50 da ake yi a kungiya zai koma 60 nan gaba