Gerard Houllier: Liverpool ta cancanci a ba ta kofin Premier na bana

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kocin Liverpool, Gerard Houllier ya ce ya kamata a bai wa Liverpool kofin Premier bana koda ba a kammala wasanni ba saboda cutar korona.
Liverpool tana mataki na daya a kan teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da ta biyu Manchester City, kuma sauya wasa tara a karkare kakar 2019-20.
Ranar 9 ga watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin tamaula a Ingila don gudun yada cutar korona.
Houllier wanda ya ja ragamar Liverpool ta lashe FA CUP da Uefa a 2001 a kaka shida da ya yi a kungiyar ya ce Liverpool ta cancanci a damka mata kofin Premier na shekarar nan.
Rabon da Liverpool ta lashe kofin Premier tun 1990, kuma Houllier ya ce an bai wa Paris St Germain kofin Faransa na bana da tazarar maki 12, ya kamata a bai wa Liverpool na Premier wadda wasa biyu take fatan ci ta zama gwarzuwar gasar bana.
Houllier wanda ke aikin mai bai wa shugaban kungiyar Olympique Lyon, Jean-Michel Aulas shawara ya kara da cewar ya kamata a jira kan hukuncin da gwamnati za ta yanke ko ya kamata a ci gaba da wasanni ko akasin hakan.







