Magajin birnin Liverpool na tsoron abinda zai faru in an koma buga Premier

Asalin hoton, Getty Images
Magajin Birnin Liverpool, Joe Anderson ya ce yana fargabar kar a bar baya da kura idan an ci gaba da Gasar Premier.
Anderson ya ce magoya bayan Liverpool za su taru makil a wajen filin Anfield, balle ma a ce kungiyar ta lashe kofin kakar 2019-20.
Mahukuntan Gasar Premier sun sanar da kungiyoyi cewar sai filin da suka amince ne za a buga wasa, hakan na nufin wasu ba za su fafata ba a filinsu.
Liverpool na sa ran lashe kofin kakar nan kuma karo na farko tun bayan shekara 30, inda take ta daya a kan teburi da tazarar maki 25 tsakaninta da Manchester City ta biyu.
Ana sa ran ci gaba da Gasar cin kofin Premier ranar 8 ga watan Yuni, bayan da ake sa ran 'yan wasa su fara motsa jiki a cikin watan Mayu.
Anderson ya ce ''Ko da Liverpool za ta buga wasanta babu 'yan kallo, sai an samu wasu magoya bayan sun taru a wajen Anfield makil don mara wa kungiyar baya da jiran sakamako.''
Ya kara da cewar ''Ba dukkan magoya baya ne za su amince da kin zuwa kusa da Anfield, kuma magoya da dama za su so yin murnar lashe kofin Premier na farko tun bayan shekara 30.''
Sama da mutum 300 suka mutu a asibitin Liverpool sakamakon cutar korona.











