Ko Lewandowski zai haura Muller a cin kwallaye a Bundesliga?

Asalin hoton, Getty Images
An ci gaba da buga gasar Bundesliga tun cikin watan Mayu don karkare wasannin 2019-20 da cutar korona ta kawo tsaiko.
Kawo yanzu an buga wasa uku kuma 29 jumulla, saura karawa biyar a kammala gasar kasar Jamus ta bana.
Kawo yanzu dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski ne ke kan gaba da kwallo 29, bayan wasannin mako na 29, shin ko Lewandowski zai haura Gerd Muller a cin kwallaye a wasannin?
Lewandowski ya taba cin kwallo 26 bayan buga wasannin mako na 29 a kakar 2015-16 a kuma shekarar ce ya ci kwallo 30 jumulla ya kara yin wannan bajintar a kakar gaba.
Sai dai kuma a lokacin na biyu ya yi da tazarar kwallo daya tsakaninsa da Pierre Emerick Aubameyang a lokacin yana Borussia Dortmunda da ya ci kwallo 31 a raga.
A kakar 2017-18 ne Lewandowski ya lashe kyuatar dan wasan da ya ci kwallaye da yawa a Bundesliga mai 29 a raga sannan ya kara yin bajinta a kakar gaba da kwallo 22.
Dan wasa na karshe da ya lashe kyautar sau biyu a jere shi ne Ulf Kirsten, wanda ya taka leda a Bayern Leverkusen.
Dan wasan da ya lashe kyautar cin kwallaye a Bundesliga karo uku a jere shi ne Mullaer, wanda ya fara da zura 40 a kakar 1971-72.
Muller ya ci wa Bayern Munich kwallo 365 a gasar Bundesliga tsakanin 1964 da 1979.
.











