Robert Lewandowski ya ci gaba da jan ragama a cin kwallo a Bundesliga

Asalin hoton, Reuters
Robert Lewandowski ya ci kwallo biyu ranar Asabar a wasan da Bayern Munich ta doke Fortuna Dusseldorf 5-0 a wasan mako na 29 a gasar Bundesliga.
Tun kan hutu Bayern ta zura kwallo uku a raga, bayan da Dusseldolf ta fara cin gida, sai Benjamin Pavard da kuma Lewandowski kowanne ya ci kwallo.
Dan wasan tawagar Poland ya ci kwallo na biyu a wasan, yayin da matashin dan wasa Alphonso Davies ya ci na biyar a karawar.
Kawo yanzu Lewandowski ya ci kwallo 29 a gasar Bundesliga ta bana, kuma guda 43 da ya ci wa Bayern Muich a dukkan karawar da ya yi mata a 2019-20.
Bayern ta cinye dukkan karawar da ta buga tun lokacin da aka ci gaba da Bundesliga cikin watan Mayu, wadda aka dakatar a cikin watan Maris saboda bullar cutar korona.
Bayern wadda ke fatan lashe kofin Bundesliga na takwas a jere ta ci kwallo 13 aka zura mata biyu a raga tun lokacin da aka ci gaba da wasannin shekarar nan.
Wadanda ke kan gaba a cin kwallo a gasar Bundesliga:
- Robert Lewandowski Bayern Munich 29
- Timo Werner RB Leipzig 24
- Jadon Sancho Borussia Dortmund 14







