Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Havertz, Higuain, Pjanic, Koulibaly, Silva, Lazaro
Tsohon dan wasan Jamus Jens Nowotny ya shawarci dan wasan Bayer Leverkusen Kai Havertz, mai shekara 20, da kada ya karbi tayin da Liverpool ta yi masa na komawa can yana mai cewa maimakon hakan gara ya koma Borussia Dortmund. (Goal)
Juventus za ta iya sayar da 'yan wasa da dama, cikinsu har da dan wasan Bosnia Miralem Pjanic, mai shekara 30, da dan wasan Argentina Gonzalo Higuain, mai shekara 32, a bazara a wani bangare na shirin da kungiyar take yi na samun kudi domin rage matsin tattalin arzikin da take fama da shi sakamakon annonar korona. (Daily Mail)
Barcelona ta kara matsa lamba a yunkurin da take na sayo dan wasan Inter Milan dan kasar Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 22, da Pjanic. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Manchester United tana sake yunkurin dauko dan wasanNapoli dan kasar Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 28, bayan ta fahimci cewa Liverpool tana son dauko dan wasan. (Gazzetta dello Sport via Daily Express)
Golan Liverpool Loris Karius, mai shekara 26, ba zai koma atisaye a kungiyar ba. Dan kasar ta Jamus ya soke kwangilar aronsa a Besiktas a farkon watan da muke ciki. (Daily Star)
Dan wasan da ke zaman aro aNewcastle United Valentino Lazaro yana jiran abin da manajan daraktan kungiyar Lee Charnley zai ce game da makomarsa a kakar wasa mai zuwa. Dan wasan na Austria mai shekara 24 ya koma Newcastle United dagaInter Milan a watan Janairu. (Newcastle Chronicle)
Manchester City tana da kwarin gwiwar cewa David Silva, mai shekara 34, zai amince ya tsawaita zamansa na dan kankanen lokaci domin samun damar kammala kakar wasa ta bana. Tun asali kwangilar dan wasan tsakiyar na Spaniya za ta kare ranar 30 ga watan Yuni. (ESPN)
Manchester United za ta dawo da golan Portugal dan shekara 23, Joel Pereira, daga zaman aron da yake yi a Hearts sakamakon kammala gasar Premier ta Scotland. (Manchester Evening News)
Wolves ta tsawaita kwangilar golan Ingila mai shekara 33 John Ruddy da shekara daya. (Birmingham Mail)
Kocin Chelsea Frank Lampard yana fatan 'yan kwallonsa da kwangilarsu ta kare za su tsawaita zamansu na kankanen lokaci, zuwa karshen kakar wasa ta bana. Kwangilar dan wasan Brazil Willian, mai shekara 31, da dan wasan Faransa Olivier Giroud, mai shekara 33, za ta kare ranar 30 ga watan Yuni. (Chelsea)
Lampard ya yi watsi da damar zama kocin Ipswich saboda ba su da kudi, a cewar kanen mahaifinsa Harry Redknapp. (Sun)
Fitaccen dan wasan Roma dan kasar Italiya Francesco Totti, mai shekara 43, ya ce ya kusa komawa Real Madrid amma basu amince su ba shi albashi irin wandaRaul yake karba ba. (Libero via Marca)