Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kungiyoyin Premier League za su fara atisaye cikin rukuni ranar Talata
Kungiyoyin da ke buga Premier sun yadda cewa ranar Talata za su fara atisaye na rukunin 'yan wasa don gudun yada cutar korona.
'Yan wasa za su dinga bayar da tazara a tsakaninsu, ba a yadda su dinga hada jiki ba a lokacin motsa jikin.
An cimma wannan matsaya ne bayan da aka tattauna da 'yan wasa da koci-koci da likitocin kungiya da masana kiwon lafiya masu zaman kansu da kuma gwamnati.
Mahukuntan gasar Premier sun ce matakan kare lafiya shi ne kan gaba kuma dole a tanadi matakan kariya da na tsabtar muhalli yayin atisaye.
Za kuma a dinda tuntubar 'yan wasa da masu horar da tamaula da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki kan yadda ya kamata a gudanar da atisayen ba tare da matsala ba.
Cikin watan Yuni ake sa ran ci gaba da gasar Premier, bayan da Liverpool ke mataki na daya da tazarar maki 25 tsakaninta da Mancheshester City.
A cikin watan Maris aka dakatar da dukkan wasannin tamaula a Ingila don gudun yada cutar korona.
Ranar Alhadi aka ci gaba da gasar Bundesliga karawar mako na 25 ba tare da 'yan kallo ba.
Hakan ya sa gasar ta zama ta farko da aka ci gaba da yi tun bayan bullar annobar da ta dagula komai a duniya.
Haka kuma a gasar ta Bundesliga an yi amfani da sabuwar dokar sauya 'yan kwallo biyar a wasa, inda Schalke ta amfana da hakan a wasan da Borussia Dortmund ta doke ta 4-0 ranar Asabar.Kungiyoyin Premier sun amince su fara daukar daya daga matakan da za a bi kan yadda ya kamata a ci gaba da wasannin da suka rage na 2019-20.
Matakan da za a dauka kan a koma ci gaba da gasar Premier
- 19 May: 'Yan wasa za su fara atisaye a cikin rukuni da matakan bayar da tazara a tsakaninsu
- 25 May: Ranar karshe da Uefa ta bai wa mambobinta su sanar da ita ko za su iya karkare kakar bana
- 1 June: Ranar da gwamnati ta tsayar ta watakila a ci gaba da wasu wasanni ba tare da yan kallo ba
- 12 June: Ake sa ran ci gaba da gasar Premier League don karkare kakar 2019-20