Dan wasan Wolverhanmpton ya karya dokar hana fita

Wolverhampton Wanderers ta ce ta kwan da sanin dan wasanta Morgan Gibbs-Whites ya karya dokar hana fita, bayan da ya halarci wani biki a Landan.

Kungiyar ta ce ta dauki matakin ladabtar wa ta hanyar cikin gida ba tare da kowa ya ji ba.

A karshen mako ne aka saka wani bidiyon Gibbs-White a kafar sada zumunta a Snapchat a wurin biki, koda yake daga baya an goge shi.

A makon jiya ne dan wasan tawagar Ingila ya saka sako a kafar sada zumuntarsa cewar ya kamata kowa ya zauna a gida abi dokar da gwamnati ta sa ta hana zirga-zirga don kawo karshen yada cutar korona.

Gibbs-White mai buga wa Wolverhampton wasan tsakiya ba shi ne na farko da ya karya dokar hana fita da gwamnati ta saka ba don hana yada annobar.

Dan wasan Everton, Moise Keane na jiran hukunci da za a yanke masa, bayan da ya hada biki a gidansa.

Haka shima dan wasan Manchester City, Kyle Walker na jiran hukuncin da kungiyar za ta yi masa, bayan da ya gayyaci wasu karuwar biyu gidansa.

Mahukuntan gasar Premier League na tattauna hanyoyin da ya kamata domin a ci gaba da wasanni a cikin watan Yuni.

Ranar 13 ga watan Maris aka dakatar da wasannin Premier League, kuma saura wasa tara a karkare kakar 2019-20.